SHARHIN FILM DIN (HAFEEZ 2019)
GABATARWA
Kamfanin (Mai Shadda Investment) ne suka wallafa, AN ALI NUHU MOVIE sune suka shirya shirin, Abubakar Bashir (Mai shadda) Shine furodusan shirin, Labari ( Story) Umar M Sharif, Marubuciyar Shirin (Script Writer) Itace fitacciyar marubuciyar nan wato FAUZIYYA D. SULAIMAN, Har ila yau ALI NUHU shine Daraktan shirin.
'Yan Wasan shirin sun hada da: Ali Nuhu Wanda ya fito amatsayi (Bawa Mai Kaba) Umar M Shariff Wanda shine aka Gina film din da sunansa wato (HAFEEZ) Wanda shine Tauraruwarsa tafi haskawa acikin shirin, sauran yan wasan sun hadada: Maryam Yahaya, Yakubu Muhammad, Abba El-Mustapha, Hassan Muhammad, Bilkisu Shema, Zainab Preety, Princess Khadejat , Maryam AB Yola, Aishatu (Humairah), Rashida Mai Sa'a, Saifullahi Fulani, Da Sauransu.
Mawakan shirin Sune:
-Nura M Inuwa, Umar M Shareef, Hamisu Breaker, Abdul D.One. wakoki guda 6 ne acikin shirin.
Shirine Wanda ya kunshi Nishadantarwa, Fadakarwa, Ilimintarwa gami da wa'azantarwa acikin hikimi da kwarewa ta hanyar Nuna Rayuwa da cakudedeniya a tsakanin MAI KUDI da TALADA da kuma Takun saka ko Rashin jituwa dake tsakaninsu, Sannan Sai SOYAYYA da wanda abune dayake faruwa awannan zamani da muke ciki wanda wadancan abubuwa Ukun Sune ainihin Manyan Abubuwa da shirin Ya kunsa.
TAKAITACCEN ABINDA SHIRININ YA KUNSA ( PLOT SUMMARY)
Umar M Shareef ( Hafeez) Saurayi Dan gaye, Dan Hutu, Dan Boko, Mai Aji, Dan gidan Alhaji Muhsin Hamshakin Attajiri.
Shine kadai 'Da awajen Iyayensa shiyasa suke Matukar Kaunarsa tareda Biyema duk wani zabin zuciyarsa. Saidai Babban Burinsu shine suga dansu Hafeez Yayi Aure Tunda ya kammala Karatu, wanda shine abinda suke fata, Hakane yasa iyayensa Bangarorin biyu keta kokari Don ganin sun hadasa Aure da 'yan Mata makusantansu, wato 'yar abokin mahaifinsa wanda itama Mahaifiyarsa ke fatan ta hadasa da 'yar Kawarta, saidai shi babu Aure a zuciyarsa.
Kwanci-tashi sai Tallan 'yan Mata ake masa, sunata rububinsa amma shi ko a jikinsa.
Kwatsam! Wata Rana saiya Hadu da (Safna) yarinya mai Hankali , Biyayya ga iyaye sannan ga kamala, 'yar gidan Ali Nuhu wanda ya fito Amatsayin (Malam Sada Mai Kaba) mutum mai kima da mutunci ga gudun duniya, Sannan kuma Talaka Fitik! Wanda suke rayuwa cikin kangin Talauci da hali matsananci.
Kwanci-Tashi soyayya ta girmama har taikai ga iyayen Safna sun Bukaci ya Turo magabatansa. Hakan kuwa akayi dukda Iyayensa sun tsani ya Auri 'yar gidan Talakawa, amma suka amince sakamakon kauna da sukema Dansu.
Saidai Ranar Farko Da Mahaifin Safna yaga HAFEEZ sai yace "Sam bazai aurama Hafeez Safna ba" A sakamakon HAFEEZ ne Ya turesa da Mota Sannan yayi masa wulakanci sabida shi Talaka ne, wannan ne yasa itama Safna Tabi Ra'ayin Mahaifinta.
A Daya Bangaren kuma HAFEEZ ya shiga Damuwa matuka Asakamakon abinda ya faru, gashi iyayensa kudinsu ya kasa siya ma Dansu soyayyar Safna Awajen Mahaifinta.
Haka ayita tafiya, ga HAFEEZ yana cikin muyacin hali, daga karshe sai yayi nadamar abinda ya aikata, kuma Aka amince masa ya Auri Safna.
MANYAN DARUSSAN DA FILM DIN YA KUNSA (THEMES OF STORY)
- Karshen wulakanci da rashin Mutunci shine dana sani, domin kuwa munga abinda HAFEEZ ya shukama mahaifin Safna Kuma ya girba.
-Rashin Kyautatawar da wasu masu kudi ke yima Talakawa awannan zamani.
-Ba Kowanne Abu kudi ke siyaba, domin kuwa kudin Mahaifin HAFEEZ basu amfana masa komaiba wajen Mallakar Safnah.
-Son Maso wani Koshin wahala: babu shakka munga yadda 'yan mata keta gwara kawunansu wajen bayyana soyayyarsu ga wanda Sam bata tasu yake ba wato (HAFEEZ).
-ILLar Talla ga 'yaya mata da muhimmancin yin taka tsamtsam wajen kula da Tarbiyyarsu, kamar yadda Ali Nuhu ya kare martabar 'yarsa Safna.
-Halin Kunci da Talauci da Tabarbarewar Ilimi Awannan Kasa tamu najeriya, kamar yadda muka gani hakan ne yasa ilimi ya gagari Dan Talaka. E.t.c
FILM DIN YA FADAKAR SOSAI KU KALLESA.
06/07/2019
Lawan M Ahmad Karaye.

No comments:
Post a Comment