Sunday, August 25, 2019

RANAR HAUSAWA TA DUNIYA

.YAU CE RANAR HAUSA TA DUNIYA

Rana ce ta musamman da Majalisar Dinkin duniya ta kebe ranar don habaka harsunan duniya da raya al'adu a tsakanin al'umma.

Hakikanin gaskiya akowacce shekara ina farin ciki da wannan rana dukda kasan cewa ta ni ban gaji Hausa ba ta kowanne fanni, amma saidai na kasan ce Tamkar Bahaushe sak domin acikin hausawa aka haifeni, anan na taso na girma, Nayi abokai, sannan na koyi abubuwa marasa adadi a harshen Hausa.
-Na farko rayuwa ta ta saje data Hausawa kama daga kan saka kaya, Al'adu, mu'amalah da zamantakewar rayuwa, Kai hatta magana babu harshen dana fi iya amfani dashi kamar Hausa , kama daga kan Magana, Rubutu Da sauransu.

-Al'adun Hausawa Suna da ban sha'awa da nishadi, da koyar da darussa matuka da kuma jarumta. Daga cikin Al'adun Hausawa Na koyi abubuwa kamar haka:

-Al'adun Biki kamar (kawance, jere, kamu, Saka lalle, Wankan Amarya, Kai amarya daki, Budar kai, Tawaiga da sauransu) da Wasan Tashe, wasan Kalankuwa, Wasannin Dandali da suka hada da: (Langa-langa, wasan Burum-Burum, wasan Madundumi, da sauransu) wasan kokuwa da sauransu, Wanda wadannan abubuwa ne da hausawa sukayi suna akansu.

-Wani Abu da yake kara bani sha'awa da harshen Hausa shine: irin yadda harshen yake da dadi da kuma salon zance kala-kala , Wanda kana zaune zakaji an fadi abinda kai baka taba jiba misali kamar.

*Karin Magana
*Habaici (gugar zana)
*Zaurance.
*Zambo
*Kirari da Take.
*Ba'ah da tumasanci. Da sauransu .

Hausawa mutanene masu Neman abin duniya domin dogaro da kai, sunayin Noma, kiwo, saka, Rini, farauta, fatauci, kira , sassaka, Rini, jima, da sauransu.

A iya rayuwa ta cikin hausawa mutane ne masu kamun kai, nutsuwa, hakuri, juriya da hangen nesa.
A iya fahimtata Hausawa suna Kauye, kuma acan ne ake koyar tsantsar Hausa kuma ta ainihi da kuma Al'adun Hausa.

Ina farin cikin kasancewa a cikin Hausawa domin na koyi abubuwan da Allah kadai yasan Adadinsu.

26/08/2019
Lawan M Ahmad Karaye
07069343044

Tuesday, August 6, 2019

SHARSHIN FILM DIN (HAFEEZ 2019)

SHARHIN FILM DIN (HAFEEZ 2019)

GABATARWA

Kamfanin (Mai Shadda Investment) ne suka wallafa, AN ALI NUHU MOVIE sune suka shirya shirin, Abubakar Bashir (Mai shadda) Shine furodusan shirin, Labari ( Story) Umar M Sharif, Marubuciyar Shirin (Script Writer) Itace fitacciyar marubuciyar nan wato FAUZIYYA D. SULAIMAN, Har ila yau ALI NUHU shine Daraktan shirin.
'Yan Wasan shirin sun hada da: Ali Nuhu Wanda ya fito amatsayi (Bawa Mai Kaba) Umar M Shariff Wanda shine aka Gina film din da sunansa wato (HAFEEZ) Wanda shine Tauraruwarsa tafi haskawa acikin shirin, sauran yan wasan sun hadada: Maryam Yahaya, Yakubu Muhammad, Abba El-Mustapha, Hassan Muhammad, Bilkisu Shema, Zainab Preety, Princess Khadejat , Maryam AB Yola, Aishatu (Humairah),   Rashida Mai Sa'a, Saifullahi Fulani, Da Sauransu.
Mawakan shirin Sune:
-Nura M Inuwa, Umar M Shareef, Hamisu Breaker, Abdul D.One. wakoki guda 6 ne acikin shirin.
Shirine Wanda ya kunshi Nishadantarwa, Fadakarwa, Ilimintarwa gami da wa'azantarwa acikin hikimi da kwarewa ta hanyar Nuna Rayuwa da cakudedeniya a tsakanin MAI KUDI da TALADA da kuma Takun saka ko Rashin jituwa dake tsakaninsu, Sannan Sai SOYAYYA  da wanda abune dayake faruwa awannan zamani da muke ciki wanda wadancan abubuwa Ukun Sune ainihin Manyan Abubuwa da shirin Ya kunsa.

TAKAITACCEN ABINDA SHIRININ YA KUNSA ( PLOT SUMMARY)

Umar M Shareef ( Hafeez) Saurayi Dan gaye, Dan Hutu, Dan Boko, Mai Aji, Dan gidan Alhaji Muhsin Hamshakin Attajiri.
Shine kadai 'Da awajen Iyayensa shiyasa suke Matukar Kaunarsa tareda Biyema duk wani zabin zuciyarsa. Saidai Babban Burinsu shine suga dansu Hafeez Yayi Aure Tunda ya kammala Karatu, wanda shine abinda suke fata, Hakane yasa iyayensa Bangarorin biyu keta kokari Don ganin sun hadasa Aure da 'yan Mata makusantansu, wato 'yar abokin mahaifinsa wanda itama Mahaifiyarsa ke fatan ta hadasa da 'yar Kawarta, saidai shi babu Aure a zuciyarsa.
Kwanci-tashi sai Tallan 'yan Mata ake masa, sunata rububinsa amma shi ko a jikinsa.

Kwatsam! Wata Rana saiya Hadu da (Safna) yarinya mai Hankali , Biyayya ga iyaye sannan ga kamala, 'yar gidan Ali Nuhu wanda ya fito Amatsayin (Malam Sada Mai Kaba) mutum mai kima da mutunci ga gudun duniya, Sannan kuma Talaka Fitik! Wanda suke rayuwa cikin kangin Talauci da hali matsananci.
Kwanci-Tashi soyayya ta girmama har taikai ga iyayen Safna sun Bukaci ya Turo magabatansa. Hakan kuwa akayi dukda Iyayensa sun tsani ya Auri 'yar gidan Talakawa, amma suka amince sakamakon kauna da sukema Dansu.
Saidai Ranar Farko Da Mahaifin Safna yaga HAFEEZ sai yace "Sam bazai aurama Hafeez Safna ba" A sakamakon HAFEEZ ne Ya turesa da Mota Sannan yayi masa wulakanci sabida shi Talaka ne, wannan ne yasa itama Safna Tabi Ra'ayin Mahaifinta.
A Daya Bangaren kuma HAFEEZ ya shiga Damuwa matuka Asakamakon abinda ya faru, gashi iyayensa kudinsu ya kasa siya ma Dansu soyayyar Safna Awajen Mahaifinta.
Haka ayita tafiya, ga HAFEEZ yana cikin muyacin hali, daga karshe sai yayi nadamar abinda ya aikata, kuma Aka amince masa ya Auri Safna.

MANYAN DARUSSAN DA FILM DIN YA KUNSA (THEMES OF STORY)

- Karshen wulakanci da rashin Mutunci shine dana sani, domin kuwa munga abinda HAFEEZ ya shukama mahaifin Safna Kuma ya girba.

-Rashin Kyautatawar da wasu masu kudi ke yima Talakawa awannan zamani.

-Ba Kowanne Abu kudi ke siyaba, domin kuwa kudin Mahaifin HAFEEZ basu amfana masa komaiba wajen Mallakar Safnah.

-Son Maso wani Koshin wahala: babu shakka munga yadda 'yan mata keta gwara kawunansu wajen bayyana soyayyarsu ga wanda Sam bata tasu yake ba wato (HAFEEZ).

-ILLar Talla ga 'yaya mata da muhimmancin yin taka tsamtsam wajen kula da Tarbiyyarsu, kamar yadda Ali Nuhu ya kare martabar 'yarsa Safna.

-Halin Kunci da Talauci da Tabarbarewar Ilimi Awannan Kasa tamu najeriya, kamar yadda muka gani hakan ne yasa ilimi ya gagari Dan Talaka. E.t.c

FILM DIN YA FADAKAR SOSAI KU KALLESA.

06/07/2019
Lawan M Ahmad Karaye.

Thursday, August 1, 2019

FAGEN TARIHIN KWALLON KAFA

.MAFI AKASARIN 'YAN KWALLON DA SUKA SHAHARA ADUNIYA ASALINSU TALAKAW NE.

Tabbas Masu iya magana sunyi gaskiya da sukace "Idan kaji wane ba banza ba" wannan haka yake, iya nazari da binciken danayi dangane da rayuwar 'yan wasan kwallon kafa na duniya na yanzu da na da, sai naga cewar mafi akasarin fitattun 'yan wasa wadanda suka sami mashahuranci a fagen kwallon kafa kamar irinsu Pele, Ronaldo, Messi e.t.c dukkansu sun taso ne cikin wani yanayi mai tsanani inda daga bisani kuma sune abin kallo da kwatance akwallon kafa tun daga kafiwarta zuwa yanzu.

BARI MU KALLI TARIHIN RAYUWAR PELE, TSOHON DAN WASAN BRAZIL

Asalin sunansa shine (Edson Arantes do Nascimento), wanda aka fi sani a duniya da suna Pelé, an haife shi ne ranar 23 ga watan oktoba a wani karamin gari mai suna Três Corações a yankin Minas Gerais dake  Kasar Brasil.
Bayan an haife shi, iyayensa sun yi bikin rad'a masa suna da (baptisma) a wata chochi wadda a ke kira (Igreja da Sagrada Familia de Jesus, Maria e José).Sunan  Mahaifinsa João Ramos do Nascimento ko kuma Dondinho, watau sunan da aka bashi a Lokacin zamaninsa shi ma ya buga k'wallon k'afa na rukuni-rukuni. Ya yi babban domin irin gwanintar da ya nuna ta fannin buga k'wallon kafa; musamman buga kwallo da kai. Ya yi wasan 'dan tsakiyar fili tare da wata kungiyar kwallon kafa mai suna Fluminense har zuwa lokacin da ya sami wata raunin da ya dakatar da shi daga cin gaba da buga k'wallon kafa a gasar rukuni-rukuni.
Sunan mahaifiyarsa Celeste. Ta girmar da Pelé da sauran 'ya'yanta cikin kyakyawar tarbiya da soyaya mai yawa.

A lokacin da ya ke yaro kankani, Pelé da iyayensa sun k'aura zuwa wani gari mai suna Baurú a tsakiyancin jihar São Paulo a k'asar Brasil.
A wannan garin ne ya fara koyan hikimar wasan kwallon kafa (a harshen Portugal-Brasil, watau futebol), har ya gwanance. Shi da kansa ya taba cewa "tinha três corações" fassaran wannan karin magana shi ne wai ya na da zuchiyoyi guda uku.
Ya na magana ne a kan garuruwa guda uku da ya rike mafi kusa da zuchiyarsa watau garin da aka haife shi, Três Corações, da birnin Baurú da kuma Santos.

-

SANA'OIN PELE

Da farko dai sana'ar da Pelé ya fara yi, (Shoe shinier) ne watau mai goge takalma. Amma ya na sha'awar buga k'wallon k'afa har cikin mafarkinsa Pelé ya fara buga k'wallon k'afa tun yana kurchiyarsa. Bayan da ya yi wasa da wa'dansu kananan k'ungiyoyin k'wallo kamar su Baquinhoda kuma Sete Setembro, ya kuma fara buga k'wallon k'afa a wata kulob mai suna Ameriquinha.
Wannan kulob ba ta da kwatch(watau mai horan 'yan wasa). A wannan lokacin ne fa, yana da shekaru goma sha 'daya kawai, kuma wani shahararan 'dan buga k'wallo na k'asar Brasil mai suna Waldemar de Brito ya ga irin basira da kok'arin da Pelé ya nuna a wasar k'wallon k'afa.
De Brito ya gane cewa lallai ya kamata ya gayyaci wannan matashi zuwa kungiyar k'wallon k'afa wanda shi De Brito ke neman ya fara. (Sunan kungiyar Clube Atlético Baurú?) A 1956, Pelé ya cika shekaru goma sha biyar da haihuwa a duniya.
A lokacin ne kuma de Brito ya gayyace shi zuwa babban birnin São Paulo domin gwadawar wasan kwallo na a tsinto a fitar domin shiga k'ungiyar wasan kwallo mai muhiminci wanda ake kira Santos Futébol Clube (SFC). Rannan da ya fara wasa, de Brito ya fada wa masu horan yan wasa a wannan k'ungiyar cewa "wannan yaro (watau Pelé) zai zama babban zakaran cikin kwararun 'yan buga k'wallon k'afa a duk duniya nan gaba".

Tabbas a yanzu shine Dan kwallon da duniya tafi kallo amatsayin Wanda yafi kowanne taka rawar gani a fagen kwallon kafa tun daga sanda aka kirkireta zuwa yanzu, kuma sunansa shine a farko cikin kundin tarihin kwallon kafa na duniya Dana kasar Brazil Wanda har abada baza'a manta dasu ba.

07069343044

TABARBAREWAR ILIMI A NAJERIYA

DALILAN DA SUKASA ILIMI YA TABARBARE A NIGERIA🇳🇬

Duniya ta yarda ta amince cewar, babu wani aiki dayake da muhimmanci irin aikin koyarwa munaso ko bamaso domin kuwa a makarantane ake samarda silar taka kowanne mataki dayake da muhimmanci kama daga kan likitoci,injiniyoyi, alkalai, 'yan siyasa, 'yan kasuwa Dasauransu duk suna karkashin malami.
Amma saidai wani abun mamaki da takaici harkar koyarwa itace koma baya awannan kasa, wanda zamu iya danganta hakan da wadannan dalilai:

-Na farko wannan matsalar kaso 80% daga gwamnatine wanda itace ta cirema al'umma sha'awar aikin koyarwa sabida halin burus da take yima fannin.
Ba'a warema harkar ilimi kaso mafi tsoka da za'a kulada fannin kama daga kan muhallinda dalibai zasu zauna su koyi karatu da samarda isassun kayan aiki da zasu taimakawa malamai da dalibai , gashi malamai basa samun albashi yadda ya kamata, albashinsu ko abinci baya biya masu bare sauran hidimar yau da kullum kawai ana dan tsutsura masu ne, Akarkashin wannan ya haifarda rashin koyarwa yadda ya kamata, Rashin zuwa makaranta akan lokaci, sa6ama ka'idar koyo da koyarwa daga kan malamai zuwa dalibai, acikin wannan yanayi ne yasa dalibai basa samun tushe karatu mai kyau.

Bugu-da-kari wancan dalili ya haifarma dalibai rashin sha'awa na harkar koyarwa, idan zaka tambayi dalibai dari abinda sukeso su zama bazaka sami guda 5 da zasu za6i aikin koyarwa ba.

Mafi akasarin daliban dake karatu a kwalejojin koyarda ilimi a wannan kasa kaso 99% ba asan ransu suke shigarta ba, suna shigane sabida karancin guraben karatu da muke dasu da wahalar samun adimishin a jami'o'i, kai in takaice maka labari suma mafi akasari basa fatan su zama malamai sabida wadancan matsaloli dana lissafa. a haka aketa tafiya awannan kasa.

-Sannan suma iyaye suna bada gudunmawa wajen lalacewar ilimi awannan kasa, dalilina shine:
- rashin ko in kula ga iyayen yara musamman na kauyaku, basa kula da suturar yara, basa basu tallafi akaratunsu yadda ya kamata, basa bibiyar makarantun 'yayansu da tsarin yadda ake karantarda 'yayansu, basa tuntubar yaro idan ya dawo gida bare su taimaka masa da HOME WORK & EXTRA LESSON domin bunkasa ilimin dansu da sauransu.

Gwamti bata bawa abun muhimmanci ba, malamai basason harkar, dalibai suma basaso, a tunaninka ta yaya kake ganin za'a magance wadannan matsaloli?


MANHAJAR FACEAPP

WACCE BARAZANA CE KE TATTARE DA MANHAJAR FACEAPP??

Masu amfani da shafukan sada zumunta na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan manhajar FaceApp- manhajar da ke sauya hotunan fuskokin mutane ta nuna su da yarinta ko tsufa.
Dubban mutane na ta nuna sakamakon amfani da manhajar a shafukansu na sada zumunta.
Amma tun da manhajar ta bazu a 'yan kwanakin nan, wasu sun nuna damuwarsu kan sharuddanta.
A ganinsu, kamfanin da ya samar da manhajar bai dauki bayanan masu amfani da ita da muhimmanci ba, amma kamfanin FaceApp ya ce ya cire mafi yawan hotunan daga rumbunsa na intanet sa'o'i 48 bayan dora su.
Haka kuma, kamfanin ya ce hotunan da masu amfani da manhajar suka zaba da kansu ne kawai yake aiki da su ba duka hotunan da ke kan waya ba.

MECECE MANHAJAR (FACEAPP)?

Manhajar FaceApp ba sabuwa ba ce. Shekaru biyu da suka gabata aka fito da ita inda take iya sauya kalar fatar mutum.
Wannan ya jawo ce-ce-ku-ce sosai kuma ya ja aka sauke manhajar.
Manhajar na iya sauya dakakkiyar fuska zuwa mai murmushi. Kuma yana iya sauya kwalliya ma.
Ana iya yin duka wannan ne tare da taimakon basirar na'urori wato Artificial Intelligence. Wasu bayanai na daukar hoton fuska sannan ya daidaita shi da wata basira da ke iya sauya kamanni.
Wannan na bayar da damar a sa murmushi ta hanyar motsa baki, da haba da kumatu don nuna kamar na gaske ne.

A INA MATSALAR TAKE NE?

An nuna damuwa a baya-bayan nan lokacin da mai samar da manhaja Joshua Nozzi ya wallafa sako a shafinsa na Twitter yana cewa FaceApp na dora hotuna da dama na mutane daga wayoyinsu na hannu ba tare da izininsu ba.
Sai dai, wani mai bincike kan harkokin tsaron shafukan sada zumunta dan Faransa ya ce babu wata damuwa a tattare da amfani da manhajar.
FaceApp ta fitarda bayanin cewa hotunan da masu amfani suka bayar da dama ne kawai manhajar ke amfani da su.

KO MASU AMFANI DA MANHAJAR SUNSAN BARAZANAR DAKE TATTARE DA ITA?

Ga wasu, wannan ita ce babbar matsalar. Manufar manhajar ta tsare bayanan mutane ta nuna cewa ana iya amfani da bayanan wasu mutanen don aika musu da talla.
Masani a harkokin intanet Mista Walshe ya shaida wa BBC cewa an yi haka ne a wata hanya da ba lallai a gane ba.

Sharuddan amfani da FaceApp sun bai wa kamfanin damar yin duk abin da suka ga dama da hotunan masu amfani da ita, wanda abin damuwa ne amma ba abin mamaki ba," in ji Dakta Murdoch.
"Kamfanoni sun san cewa kusan babu wanda yake karanta manufofin tsare bayanai don haka su kan sake abubuwa da yawa a cikin sharuddan ko da ba sa bukatarsu yanzu."

ME FACEAPP KE CEWA?

Mista Goncharov ya fitar da wata sanarwa dake cewa FaceApp na daukar hotunan da masu amfani suka zaba.
"Ba ma daukar wasu hotunan," a cewarsa.
"Za mu iya ajiye wa a rumbun mu.
"Dalilin hakan kuwa shi ne don gyara aikinmu da yadda mutane ke rububin manhajar: mun aso mu tabbatar da cewa masu amfani da manhajar ba su sa hoto daya sau da yawa ba."
"Muna cire mafi yawan hotuna daga rumbunmu cikin sa'o'i 48." a cewarsa.

DAN UWA SHIN MENENE RA'AYINKA DANGANE DA WANNAN MANHAJA TA (FACEAPP)?