Friday, September 11, 2020

CAKWAKIYAR DAKE CIKIN SHIRIN (LABARINA) MAI DOGON ZANGO.




A gaskiya na daɗe banga shirin Hausa mai matuƙar daukar hankali ba kamar wannan shiri mai dogon zango wato "Labarina" ba duba da yadda aka ginasa a bisa tsarin da yazo daidai da zamani musamman rayuwar da muke ciki a halin yanzu, a duk sati yana zuwa da sabon abu wanda za'a tattauna akansa. Lallai asanina ma tun kafuwar kannywood ban taɓa jin wani shiri  da suke yi  wanda hankalin al'umma ya koma kanasa kamar LABARINA ba, kuma duk ƙarshen episode masu kallo suna muradin zagayowar mako acikin gaggawa domin ganin cigaba.


Tafiya tayi tafiya a cikin wannan shiri, saidai lamari kullum ƙara ƙamari yake a ɓangaren soyayyar Sumayya da mahmud, da kuma matsayin soyayyar Lukman da sumayya wanda dole mu kalli abun ta fuska biyu. 


1. Gaskiya dai akwai babbar matsala a tattare da soyayyar Mahmud da sumayya duba da irin yadda take yin tafiyar hawainiya kwan gaba kwan baya, Saboda ita sumayya tana fuskantar matsala daga mahaifiyar ta, sannan shima Mahmud yana fuskantar hakan wanda takai ga iyayen nasu sunci alwashin tsine masu akan haka juna su. mahaifinta, sannan ga maganar da maigari yafurtawa dansa game da sumayya. Bayan haka mahmud akwai wani abu da yake boye tsakanin mahaifiyar sa da ƙawarta Wanda idan aka faɗa masa tabbas rayuwarsa zata tawarwatse ko ya shiga wani matsanancin hali wanda zai shiga cikin ruɗani da damuwa da dole zai Amince da soyayyar Murja. Amma a haƙiƙanin gaskiya Mahmud shine mutum na farko da yafara taimakonta a rayuwa alokacin da take tsananin neman taimako kuma yayi mata a lokacin da ya dace, kuma shi muhammud ya taimake ta ne  tsakanin sa da Allah, badan yana sonta ba, domin kuwa alokacin daya siya mata magani bai fara sonta ba sai daga bisani yafara sonta, shi kuma lukuman sai da ya tsunduma cikin sonta sannan yafara taimakonta badan komai ba sai dan ya sami matsuguni a zuciyar ta.


2. A ɓangaren Lukman kuwa shima yana kan tsari mai kyau domin ganin ya mallaki zuciyar Sumayya, kuma alamu ne dake nuna cewa yana sonta ne domin Allah kuma duk abinda yayi mata yafi ƙarfinsa duba da matsayinsa acikin shirin, ko babu komai kyauta da haƙuri, tarairaya da tausasawa sune ginshiƙin cin ribar soyayya, Lukman baya son yaji an aibata sumayya ko yayane, idan muka kalli wannan abubuwa To babu shakka Lukman bashi da wani abu, kuma shine irin majaje da kowace mace ke fatan ta aura, sannan kuma irinsa ne iyaye ke fatan ƴaƴansu su aura domin samun dawwamammen farin ciki a rayuwa.


Koda Ace  sumayya ta Auri mahmud zatayi rayuwa ne cikin tsangwama da takaici a wajen mahaifiyarsa. Sannan idan muka duba Irin wannan kishin da mahmud yakeyi ya wuce hankali a sakamakon rashin iya soyayya da rashin yarda dakai da maida hankali wajen ganin yayi mata abubuwa da zata sanya ta ƙara kusanta dashi tunda dama can shine gwarzo a wajen ta, kuma ta lallaɓa Lukman ne domin suyi rabuwa ta mutunci ba don ta fafitasa akan Mahmud ba, kowanne lokaci baya iya sarrafa zuciyar sa ya yaɗa Manufarsa cikin hikima da tausasawa, saidai ya dinga ƙoƙarin tayar mata da hankali baya tunanin wannan zai iya jefa rayuwarta a cikin matsala, kuma irin wannan kan saka mata acikin wani yanayi na fargaba koma halaka baki daya. 

Duba da waɗannan abubuwa, Babu Wanda Ya Dace Sumayya Ta Aura Sama da Lukman, domin yana sonta, yana tausayinta, baya son ɓacin ranta domin ka duba yadda yake Binta dukda Arziƙi da suke dashi, sannan yana tausayinta. 


Shiri ya ɗauki zafi, kuma yana kyau, Lallai Aminu Saira yana ƙwarewa, kuma da alamu zai cigaba da tafiyar da shirin cikin tsari duba da gogaggun ƴan wasa irinsu Nafisat Abdullahi da aka ɗora a tsarin. 


11/09/2020 

Lawan M Ahmad Karaye

Tuesday, June 16, 2020

THE FINAL DESTINATION.


Kabir Salisu He was a gentleman from exclusive to assemblage.
Clean favored and relate to the all.
He was always Human when he talked.
Now Gone far away into the final destination.

He was braver than we believe.
And stronger than you seem.
And smarter than you think.
But the most crummy  is, now we're apart…

We don't cry because our loved one is dead.
we cry because we won't ever see or talk to you.
Sunday  Is your closing day.
One day I’ll take your journey.

For my seek – turn again to life and smile.
Bu I know you gone forever.
I remain here beside you.
To speak to God in order to forgive you.

Each night I shed a silent tear.
The death shall have no dominion.
Just think of you as resting from the sorrows and the tears.
In a place of warmth and comfort.
Where there are no days and years.

~Lawan M Ahmad Karaye.

Friday, April 3, 2020

Hattara dai jama'a ya kamata a kula


Akwai kokarin zamba da ke gudana a Najeriya tun bayan barkewar cutar Coronavirus, game da batun banki a kan BVN, ana ta yaɗa saƙonni na wata mahaɗa wato (links) musamman a dandalin WhatsApp inda inda ake umartar mutane dasu danna wasu hanyoyin domin samun wasu kudade  da sunan tallafin  Gwamnatin da ake tunanin zata bada domin ragewa al'umma raɗaɗi.

 Gaskiyar magana itace "Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yanke shawarar taimakawa 'yan ƙasa da wani ɗan abinda ba'a rasa ba a sakamakon rufe kasuwanni da sauran harkar kasuwanci da hakan  ta sanya rayuwa cikin wahala ga galibin al'ummar ƙasar.

 Sun fitar da Naira dubu 8500 ga kowane ɗan ƙasa da ke da BVN. "
 Don haka mutane , ayi watsi da irin waɗancan saƙonni na WhatsApp kuma kada a bayyana BVN ɗinku ga kowane mutum ko shigar da ita a  kowane waje, domin babu alaƙar tura kuɗi da BVN kamar yadda duk mai hulɗa da banki ya sani.

Ya kamata mu sani cewa BVN katin ID ɗin kuɗin mu ne, duk wanda kaji ya tambaye ka to  yana so ya sami damar yin amfani da shi don samun duk bayanan ku na kuɗin ku, kuma yayi amfani da shi don dalilai na zamba.

 Tare da BVN ɗinka, masu zamba za su iya samun lambar asusunku, lambar wayar da kuke amfani da ita OTP da sauran bayanan ku na kuɗi.  Tare da waɗannan cikakkun bayanai, za su  ɗauki lamuni a madadinku ba tare da saninka ba, ayi amfani da katunan ATM  don siyan abubuwa ta kan layi har ma suna cire kuɗin ko su chanja su   daga ma'ajiyarku zuwa wata.

 Ka Tabbatar da cewa ka kare BVN dinka, hakane zai iya kiyaye maka damuwa ta fannin kuɗin daka adana.
Kai koda mutum ne zai tura maka kuɗi kaji ya ambaci ka basa BVN, to wallahi mazambaci ne, abubuwa biyu kacal ake buƙata. Lambarka ta asusu (Account number) sai sunan banki, shi kansa sunan asusu ana faɗa ne domin cire kokwanto. Sabida haka ya kamata jama'a mu kula, domin masu hikima sunce "son banza ke sa gidan yari cika"

03/04/2020
Lawan M Ahmad Karaye.
Email: lawanmusaahmad@gmail.com

Sunday, November 3, 2019

CIKAR BURIN MASOYA AURE

ZUWA GA (ZAINAB AHMAD) : CIKAR BURIN MASOYA AURE.

Jiya na karɓi Sakon Goron gayyata ga wata baiwar Allah mai suna (Zainab Ahmad) wacce muka kwashe kimanin shekaru 5 muna tare da ita amma da sunan zumunci, ta kan zo gidan mu nima naje gidan su mu gaisa, saidai zuciyoyin mu sun dauki abun a matsayin abota. A iya wadannan shekaru bamu taɓa yin hirar soyayya ba face hirar karatu ko sha'anin rayuwa, kai a karshe ma muka zama tamkar 'yan uwa na jini, domin kuwa mukan tattauna akan matsalolin da suka shafe mu sannan mu bawa juna shawara ta gari.

Zainab itace mace ta farko dana fara amincewa da ita a rayuwa ta kuma har na saki jiki da ita muka ɗauki lokaci mai tsawo muna gaisa, kuma muka dauki juna tamkar 'yan uwa na jini wanda ba kasafai hakan ya fiya faruwa ba a wannan zamani.
Zainab Ahmad, Itace kadai mace da nake bawa lokacina mai yawa  kasancewar ta ta daban, mai hankali, Ilimi, tunani da sanin ya kamata. Da Ace anayin zaben gwarzon abokan arziki a cikin mata to babu shakka Zainab ce zata zama Gwarzuwa a Rayuwa ta, saidai duk da haka na bata wannan kambu.

Lokaci Bazai bani damar na bayyana irin alkhairin wannan baiwar Allah ba, saidai zuciya ta shaida ce.
Sai dai kash! Bazan sami halartar shagulgulan bikin ta ba koda guda daya ba a sakamakon wata tafiya da nayi ta bazata, kuma bazan dawo ba sai bayan wannan biki.
Zuciya ta tayi matuƙar takaici na rashin kasancewa ta awannan ranar da zan taya 'yar uwata farin ciki na cikar burin ta da kuma mu baki daya. Ina ma Ace ina nan za'ayi, koda yake yaya na iya, haka Allah ya ƙaddara.

A karshe ina yima Zainab Ahmad farin cikin samun miji kuma ina taya ta farin cikin ganin wannan rana, sannan sakonnina na addu'oi da fatan alkhairi ba zasu taɓa gushewa ba.
Allah ya sanya alkhairi ya ƙara lafiya da zaman lafiya da zuriya mai amfani.
Ya Ubangiji ina riƙo da tawassali da Sunayenka tsarkaka da Manzonka manzon Rahama Annabi Muhammad (S.a.w) ka sanyama wannan aure albarka, ka tsare sharrin dake cikin sa, kasa ya zama aure na mutu ka raba.

"Tabbas cikar burin masoya shine aure".

Sunday, August 25, 2019

RANAR HAUSAWA TA DUNIYA

.YAU CE RANAR HAUSA TA DUNIYA

Rana ce ta musamman da Majalisar Dinkin duniya ta kebe ranar don habaka harsunan duniya da raya al'adu a tsakanin al'umma.

Hakikanin gaskiya akowacce shekara ina farin ciki da wannan rana dukda kasan cewa ta ni ban gaji Hausa ba ta kowanne fanni, amma saidai na kasan ce Tamkar Bahaushe sak domin acikin hausawa aka haifeni, anan na taso na girma, Nayi abokai, sannan na koyi abubuwa marasa adadi a harshen Hausa.
-Na farko rayuwa ta ta saje data Hausawa kama daga kan saka kaya, Al'adu, mu'amalah da zamantakewar rayuwa, Kai hatta magana babu harshen dana fi iya amfani dashi kamar Hausa , kama daga kan Magana, Rubutu Da sauransu.

-Al'adun Hausawa Suna da ban sha'awa da nishadi, da koyar da darussa matuka da kuma jarumta. Daga cikin Al'adun Hausawa Na koyi abubuwa kamar haka:

-Al'adun Biki kamar (kawance, jere, kamu, Saka lalle, Wankan Amarya, Kai amarya daki, Budar kai, Tawaiga da sauransu) da Wasan Tashe, wasan Kalankuwa, Wasannin Dandali da suka hada da: (Langa-langa, wasan Burum-Burum, wasan Madundumi, da sauransu) wasan kokuwa da sauransu, Wanda wadannan abubuwa ne da hausawa sukayi suna akansu.

-Wani Abu da yake kara bani sha'awa da harshen Hausa shine: irin yadda harshen yake da dadi da kuma salon zance kala-kala , Wanda kana zaune zakaji an fadi abinda kai baka taba jiba misali kamar.

*Karin Magana
*Habaici (gugar zana)
*Zaurance.
*Zambo
*Kirari da Take.
*Ba'ah da tumasanci. Da sauransu .

Hausawa mutanene masu Neman abin duniya domin dogaro da kai, sunayin Noma, kiwo, saka, Rini, farauta, fatauci, kira , sassaka, Rini, jima, da sauransu.

A iya rayuwa ta cikin hausawa mutane ne masu kamun kai, nutsuwa, hakuri, juriya da hangen nesa.
A iya fahimtata Hausawa suna Kauye, kuma acan ne ake koyar tsantsar Hausa kuma ta ainihi da kuma Al'adun Hausa.

Ina farin cikin kasancewa a cikin Hausawa domin na koyi abubuwan da Allah kadai yasan Adadinsu.

26/08/2019
Lawan M Ahmad Karaye
07069343044

Tuesday, August 6, 2019

SHARSHIN FILM DIN (HAFEEZ 2019)

SHARHIN FILM DIN (HAFEEZ 2019)

GABATARWA

Kamfanin (Mai Shadda Investment) ne suka wallafa, AN ALI NUHU MOVIE sune suka shirya shirin, Abubakar Bashir (Mai shadda) Shine furodusan shirin, Labari ( Story) Umar M Sharif, Marubuciyar Shirin (Script Writer) Itace fitacciyar marubuciyar nan wato FAUZIYYA D. SULAIMAN, Har ila yau ALI NUHU shine Daraktan shirin.
'Yan Wasan shirin sun hada da: Ali Nuhu Wanda ya fito amatsayi (Bawa Mai Kaba) Umar M Shariff Wanda shine aka Gina film din da sunansa wato (HAFEEZ) Wanda shine Tauraruwarsa tafi haskawa acikin shirin, sauran yan wasan sun hadada: Maryam Yahaya, Yakubu Muhammad, Abba El-Mustapha, Hassan Muhammad, Bilkisu Shema, Zainab Preety, Princess Khadejat , Maryam AB Yola, Aishatu (Humairah),   Rashida Mai Sa'a, Saifullahi Fulani, Da Sauransu.
Mawakan shirin Sune:
-Nura M Inuwa, Umar M Shareef, Hamisu Breaker, Abdul D.One. wakoki guda 6 ne acikin shirin.
Shirine Wanda ya kunshi Nishadantarwa, Fadakarwa, Ilimintarwa gami da wa'azantarwa acikin hikimi da kwarewa ta hanyar Nuna Rayuwa da cakudedeniya a tsakanin MAI KUDI da TALADA da kuma Takun saka ko Rashin jituwa dake tsakaninsu, Sannan Sai SOYAYYA  da wanda abune dayake faruwa awannan zamani da muke ciki wanda wadancan abubuwa Ukun Sune ainihin Manyan Abubuwa da shirin Ya kunsa.

TAKAITACCEN ABINDA SHIRININ YA KUNSA ( PLOT SUMMARY)

Umar M Shareef ( Hafeez) Saurayi Dan gaye, Dan Hutu, Dan Boko, Mai Aji, Dan gidan Alhaji Muhsin Hamshakin Attajiri.
Shine kadai 'Da awajen Iyayensa shiyasa suke Matukar Kaunarsa tareda Biyema duk wani zabin zuciyarsa. Saidai Babban Burinsu shine suga dansu Hafeez Yayi Aure Tunda ya kammala Karatu, wanda shine abinda suke fata, Hakane yasa iyayensa Bangarorin biyu keta kokari Don ganin sun hadasa Aure da 'yan Mata makusantansu, wato 'yar abokin mahaifinsa wanda itama Mahaifiyarsa ke fatan ta hadasa da 'yar Kawarta, saidai shi babu Aure a zuciyarsa.
Kwanci-tashi sai Tallan 'yan Mata ake masa, sunata rububinsa amma shi ko a jikinsa.

Kwatsam! Wata Rana saiya Hadu da (Safna) yarinya mai Hankali , Biyayya ga iyaye sannan ga kamala, 'yar gidan Ali Nuhu wanda ya fito Amatsayin (Malam Sada Mai Kaba) mutum mai kima da mutunci ga gudun duniya, Sannan kuma Talaka Fitik! Wanda suke rayuwa cikin kangin Talauci da hali matsananci.
Kwanci-Tashi soyayya ta girmama har taikai ga iyayen Safna sun Bukaci ya Turo magabatansa. Hakan kuwa akayi dukda Iyayensa sun tsani ya Auri 'yar gidan Talakawa, amma suka amince sakamakon kauna da sukema Dansu.
Saidai Ranar Farko Da Mahaifin Safna yaga HAFEEZ sai yace "Sam bazai aurama Hafeez Safna ba" A sakamakon HAFEEZ ne Ya turesa da Mota Sannan yayi masa wulakanci sabida shi Talaka ne, wannan ne yasa itama Safna Tabi Ra'ayin Mahaifinta.
A Daya Bangaren kuma HAFEEZ ya shiga Damuwa matuka Asakamakon abinda ya faru, gashi iyayensa kudinsu ya kasa siya ma Dansu soyayyar Safna Awajen Mahaifinta.
Haka ayita tafiya, ga HAFEEZ yana cikin muyacin hali, daga karshe sai yayi nadamar abinda ya aikata, kuma Aka amince masa ya Auri Safna.

MANYAN DARUSSAN DA FILM DIN YA KUNSA (THEMES OF STORY)

- Karshen wulakanci da rashin Mutunci shine dana sani, domin kuwa munga abinda HAFEEZ ya shukama mahaifin Safna Kuma ya girba.

-Rashin Kyautatawar da wasu masu kudi ke yima Talakawa awannan zamani.

-Ba Kowanne Abu kudi ke siyaba, domin kuwa kudin Mahaifin HAFEEZ basu amfana masa komaiba wajen Mallakar Safnah.

-Son Maso wani Koshin wahala: babu shakka munga yadda 'yan mata keta gwara kawunansu wajen bayyana soyayyarsu ga wanda Sam bata tasu yake ba wato (HAFEEZ).

-ILLar Talla ga 'yaya mata da muhimmancin yin taka tsamtsam wajen kula da Tarbiyyarsu, kamar yadda Ali Nuhu ya kare martabar 'yarsa Safna.

-Halin Kunci da Talauci da Tabarbarewar Ilimi Awannan Kasa tamu najeriya, kamar yadda muka gani hakan ne yasa ilimi ya gagari Dan Talaka. E.t.c

FILM DIN YA FADAKAR SOSAI KU KALLESA.

06/07/2019
Lawan M Ahmad Karaye.

Thursday, August 1, 2019

FAGEN TARIHIN KWALLON KAFA

.MAFI AKASARIN 'YAN KWALLON DA SUKA SHAHARA ADUNIYA ASALINSU TALAKAW NE.

Tabbas Masu iya magana sunyi gaskiya da sukace "Idan kaji wane ba banza ba" wannan haka yake, iya nazari da binciken danayi dangane da rayuwar 'yan wasan kwallon kafa na duniya na yanzu da na da, sai naga cewar mafi akasarin fitattun 'yan wasa wadanda suka sami mashahuranci a fagen kwallon kafa kamar irinsu Pele, Ronaldo, Messi e.t.c dukkansu sun taso ne cikin wani yanayi mai tsanani inda daga bisani kuma sune abin kallo da kwatance akwallon kafa tun daga kafiwarta zuwa yanzu.

BARI MU KALLI TARIHIN RAYUWAR PELE, TSOHON DAN WASAN BRAZIL

Asalin sunansa shine (Edson Arantes do Nascimento), wanda aka fi sani a duniya da suna Pelé, an haife shi ne ranar 23 ga watan oktoba a wani karamin gari mai suna Três Corações a yankin Minas Gerais dake  Kasar Brasil.
Bayan an haife shi, iyayensa sun yi bikin rad'a masa suna da (baptisma) a wata chochi wadda a ke kira (Igreja da Sagrada Familia de Jesus, Maria e José).Sunan  Mahaifinsa João Ramos do Nascimento ko kuma Dondinho, watau sunan da aka bashi a Lokacin zamaninsa shi ma ya buga k'wallon k'afa na rukuni-rukuni. Ya yi babban domin irin gwanintar da ya nuna ta fannin buga k'wallon kafa; musamman buga kwallo da kai. Ya yi wasan 'dan tsakiyar fili tare da wata kungiyar kwallon kafa mai suna Fluminense har zuwa lokacin da ya sami wata raunin da ya dakatar da shi daga cin gaba da buga k'wallon kafa a gasar rukuni-rukuni.
Sunan mahaifiyarsa Celeste. Ta girmar da Pelé da sauran 'ya'yanta cikin kyakyawar tarbiya da soyaya mai yawa.

A lokacin da ya ke yaro kankani, Pelé da iyayensa sun k'aura zuwa wani gari mai suna Baurú a tsakiyancin jihar São Paulo a k'asar Brasil.
A wannan garin ne ya fara koyan hikimar wasan kwallon kafa (a harshen Portugal-Brasil, watau futebol), har ya gwanance. Shi da kansa ya taba cewa "tinha três corações" fassaran wannan karin magana shi ne wai ya na da zuchiyoyi guda uku.
Ya na magana ne a kan garuruwa guda uku da ya rike mafi kusa da zuchiyarsa watau garin da aka haife shi, Três Corações, da birnin Baurú da kuma Santos.

-

SANA'OIN PELE

Da farko dai sana'ar da Pelé ya fara yi, (Shoe shinier) ne watau mai goge takalma. Amma ya na sha'awar buga k'wallon k'afa har cikin mafarkinsa Pelé ya fara buga k'wallon k'afa tun yana kurchiyarsa. Bayan da ya yi wasa da wa'dansu kananan k'ungiyoyin k'wallo kamar su Baquinhoda kuma Sete Setembro, ya kuma fara buga k'wallon k'afa a wata kulob mai suna Ameriquinha.
Wannan kulob ba ta da kwatch(watau mai horan 'yan wasa). A wannan lokacin ne fa, yana da shekaru goma sha 'daya kawai, kuma wani shahararan 'dan buga k'wallo na k'asar Brasil mai suna Waldemar de Brito ya ga irin basira da kok'arin da Pelé ya nuna a wasar k'wallon k'afa.
De Brito ya gane cewa lallai ya kamata ya gayyaci wannan matashi zuwa kungiyar k'wallon k'afa wanda shi De Brito ke neman ya fara. (Sunan kungiyar Clube Atlético Baurú?) A 1956, Pelé ya cika shekaru goma sha biyar da haihuwa a duniya.
A lokacin ne kuma de Brito ya gayyace shi zuwa babban birnin São Paulo domin gwadawar wasan kwallo na a tsinto a fitar domin shiga k'ungiyar wasan kwallo mai muhiminci wanda ake kira Santos Futébol Clube (SFC). Rannan da ya fara wasa, de Brito ya fada wa masu horan yan wasa a wannan k'ungiyar cewa "wannan yaro (watau Pelé) zai zama babban zakaran cikin kwararun 'yan buga k'wallon k'afa a duk duniya nan gaba".

Tabbas a yanzu shine Dan kwallon da duniya tafi kallo amatsayin Wanda yafi kowanne taka rawar gani a fagen kwallon kafa tun daga sanda aka kirkireta zuwa yanzu, kuma sunansa shine a farko cikin kundin tarihin kwallon kafa na duniya Dana kasar Brazil Wanda har abada baza'a manta dasu ba.

07069343044