Friday, April 3, 2020
Hattara dai jama'a ya kamata a kula
Akwai kokarin zamba da ke gudana a Najeriya tun bayan barkewar cutar Coronavirus, game da batun banki a kan BVN, ana ta yaɗa saƙonni na wata mahaɗa wato (links) musamman a dandalin WhatsApp inda inda ake umartar mutane dasu danna wasu hanyoyin domin samun wasu kudade da sunan tallafin Gwamnatin da ake tunanin zata bada domin ragewa al'umma raɗaɗi.
Gaskiyar magana itace "Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yanke shawarar taimakawa 'yan ƙasa da wani ɗan abinda ba'a rasa ba a sakamakon rufe kasuwanni da sauran harkar kasuwanci da hakan ta sanya rayuwa cikin wahala ga galibin al'ummar ƙasar.
Sun fitar da Naira dubu 8500 ga kowane ɗan ƙasa da ke da BVN. "
Don haka mutane , ayi watsi da irin waɗancan saƙonni na WhatsApp kuma kada a bayyana BVN ɗinku ga kowane mutum ko shigar da ita a kowane waje, domin babu alaƙar tura kuɗi da BVN kamar yadda duk mai hulɗa da banki ya sani.
Ya kamata mu sani cewa BVN katin ID ɗin kuɗin mu ne, duk wanda kaji ya tambaye ka to yana so ya sami damar yin amfani da shi don samun duk bayanan ku na kuɗin ku, kuma yayi amfani da shi don dalilai na zamba.
Tare da BVN ɗinka, masu zamba za su iya samun lambar asusunku, lambar wayar da kuke amfani da ita OTP da sauran bayanan ku na kuɗi. Tare da waɗannan cikakkun bayanai, za su ɗauki lamuni a madadinku ba tare da saninka ba, ayi amfani da katunan ATM don siyan abubuwa ta kan layi har ma suna cire kuɗin ko su chanja su daga ma'ajiyarku zuwa wata.
Ka Tabbatar da cewa ka kare BVN dinka, hakane zai iya kiyaye maka damuwa ta fannin kuɗin daka adana.
Kai koda mutum ne zai tura maka kuɗi kaji ya ambaci ka basa BVN, to wallahi mazambaci ne, abubuwa biyu kacal ake buƙata. Lambarka ta asusu (Account number) sai sunan banki, shi kansa sunan asusu ana faɗa ne domin cire kokwanto. Sabida haka ya kamata jama'a mu kula, domin masu hikima sunce "son banza ke sa gidan yari cika"
03/04/2020
Lawan M Ahmad Karaye.
Email: lawanmusaahmad@gmail.com
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment