A gaskiya na daɗe banga shirin Hausa mai matuƙar daukar hankali ba kamar wannan shiri mai dogon zango wato "Labarina" ba duba da yadda aka ginasa a bisa tsarin da yazo daidai da zamani musamman rayuwar da muke ciki a halin yanzu, a duk sati yana zuwa da sabon abu wanda za'a tattauna akansa. Lallai asanina ma tun kafuwar kannywood ban taɓa jin wani shiri da suke yi wanda hankalin al'umma ya koma kanasa kamar LABARINA ba, kuma duk ƙarshen episode masu kallo suna muradin zagayowar mako acikin gaggawa domin ganin cigaba.
Tafiya tayi tafiya a cikin wannan shiri, saidai lamari kullum ƙara ƙamari yake a ɓangaren soyayyar Sumayya da mahmud, da kuma matsayin soyayyar Lukman da sumayya wanda dole mu kalli abun ta fuska biyu.
1. Gaskiya dai akwai babbar matsala a tattare da soyayyar Mahmud da sumayya duba da irin yadda take yin tafiyar hawainiya kwan gaba kwan baya, Saboda ita sumayya tana fuskantar matsala daga mahaifiyar ta, sannan shima Mahmud yana fuskantar hakan wanda takai ga iyayen nasu sunci alwashin tsine masu akan haka juna su. mahaifinta, sannan ga maganar da maigari yafurtawa dansa game da sumayya. Bayan haka mahmud akwai wani abu da yake boye tsakanin mahaifiyar sa da ƙawarta Wanda idan aka faɗa masa tabbas rayuwarsa zata tawarwatse ko ya shiga wani matsanancin hali wanda zai shiga cikin ruɗani da damuwa da dole zai Amince da soyayyar Murja. Amma a haƙiƙanin gaskiya Mahmud shine mutum na farko da yafara taimakonta a rayuwa alokacin da take tsananin neman taimako kuma yayi mata a lokacin da ya dace, kuma shi muhammud ya taimake ta ne tsakanin sa da Allah, badan yana sonta ba, domin kuwa alokacin daya siya mata magani bai fara sonta ba sai daga bisani yafara sonta, shi kuma lukuman sai da ya tsunduma cikin sonta sannan yafara taimakonta badan komai ba sai dan ya sami matsuguni a zuciyar ta.
2. A ɓangaren Lukman kuwa shima yana kan tsari mai kyau domin ganin ya mallaki zuciyar Sumayya, kuma alamu ne dake nuna cewa yana sonta ne domin Allah kuma duk abinda yayi mata yafi ƙarfinsa duba da matsayinsa acikin shirin, ko babu komai kyauta da haƙuri, tarairaya da tausasawa sune ginshiƙin cin ribar soyayya, Lukman baya son yaji an aibata sumayya ko yayane, idan muka kalli wannan abubuwa To babu shakka Lukman bashi da wani abu, kuma shine irin majaje da kowace mace ke fatan ta aura, sannan kuma irinsa ne iyaye ke fatan ƴaƴansu su aura domin samun dawwamammen farin ciki a rayuwa.
Koda Ace sumayya ta Auri mahmud zatayi rayuwa ne cikin tsangwama da takaici a wajen mahaifiyarsa. Sannan idan muka duba Irin wannan kishin da mahmud yakeyi ya wuce hankali a sakamakon rashin iya soyayya da rashin yarda dakai da maida hankali wajen ganin yayi mata abubuwa da zata sanya ta ƙara kusanta dashi tunda dama can shine gwarzo a wajen ta, kuma ta lallaɓa Lukman ne domin suyi rabuwa ta mutunci ba don ta fafitasa akan Mahmud ba, kowanne lokaci baya iya sarrafa zuciyar sa ya yaɗa Manufarsa cikin hikima da tausasawa, saidai ya dinga ƙoƙarin tayar mata da hankali baya tunanin wannan zai iya jefa rayuwarta a cikin matsala, kuma irin wannan kan saka mata acikin wani yanayi na fargaba koma halaka baki daya.
Duba da waɗannan abubuwa, Babu Wanda Ya Dace Sumayya Ta Aura Sama da Lukman, domin yana sonta, yana tausayinta, baya son ɓacin ranta domin ka duba yadda yake Binta dukda Arziƙi da suke dashi, sannan yana tausayinta.
Shiri ya ɗauki zafi, kuma yana kyau, Lallai Aminu Saira yana ƙwarewa, kuma da alamu zai cigaba da tafiyar da shirin cikin tsari duba da gogaggun ƴan wasa irinsu Nafisat Abdullahi da aka ɗora a tsarin.
11/09/2020
Lawan M Ahmad Karaye

