ZUWA GA (ZAINAB AHMAD) : CIKAR BURIN MASOYA AURE.
Jiya na karɓi Sakon Goron gayyata ga wata baiwar Allah mai suna (Zainab Ahmad) wacce muka kwashe kimanin shekaru 5 muna tare da ita amma da sunan zumunci, ta kan zo gidan mu nima naje gidan su mu gaisa, saidai zuciyoyin mu sun dauki abun a matsayin abota. A iya wadannan shekaru bamu taɓa yin hirar soyayya ba face hirar karatu ko sha'anin rayuwa, kai a karshe ma muka zama tamkar 'yan uwa na jini, domin kuwa mukan tattauna akan matsalolin da suka shafe mu sannan mu bawa juna shawara ta gari.
Zainab itace mace ta farko dana fara amincewa da ita a rayuwa ta kuma har na saki jiki da ita muka ɗauki lokaci mai tsawo muna gaisa, kuma muka dauki juna tamkar 'yan uwa na jini wanda ba kasafai hakan ya fiya faruwa ba a wannan zamani.
Zainab Ahmad, Itace kadai mace da nake bawa lokacina mai yawa kasancewar ta ta daban, mai hankali, Ilimi, tunani da sanin ya kamata. Da Ace anayin zaben gwarzon abokan arziki a cikin mata to babu shakka Zainab ce zata zama Gwarzuwa a Rayuwa ta, saidai duk da haka na bata wannan kambu.
Lokaci Bazai bani damar na bayyana irin alkhairin wannan baiwar Allah ba, saidai zuciya ta shaida ce.
Sai dai kash! Bazan sami halartar shagulgulan bikin ta ba koda guda daya ba a sakamakon wata tafiya da nayi ta bazata, kuma bazan dawo ba sai bayan wannan biki.
Zuciya ta tayi matuƙar takaici na rashin kasancewa ta awannan ranar da zan taya 'yar uwata farin ciki na cikar burin ta da kuma mu baki daya. Ina ma Ace ina nan za'ayi, koda yake yaya na iya, haka Allah ya ƙaddara.
A karshe ina yima Zainab Ahmad farin cikin samun miji kuma ina taya ta farin cikin ganin wannan rana, sannan sakonnina na addu'oi da fatan alkhairi ba zasu taɓa gushewa ba.
Allah ya sanya alkhairi ya ƙara lafiya da zaman lafiya da zuriya mai amfani.
Ya Ubangiji ina riƙo da tawassali da Sunayenka tsarkaka da Manzonka manzon Rahama Annabi Muhammad (S.a.w) ka sanyama wannan aure albarka, ka tsare sharrin dake cikin sa, kasa ya zama aure na mutu ka raba.
"Tabbas cikar burin masoya shine aure".